✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto mutum 15 a gidan kangararru na bogi a Adamawa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun ceto mutum 15 tare da tsare mutum biyu a wani gidan ladabtar da kangararru mara rijista a a unguwar Wuro…

Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun ceto mutum 15 tare da tsare mutum biyu a wani gidan ladabtar da kangararru mara rijista a a unguwar Wuro Hausa wanda yake cikin Karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.

Rahotan na cewa, ‘yan sandan sun kuma mutum biyu da ake zargin sun mallaki wannan gidan kason bogi.

Aminiya tayi kokarin zantawa da kakakin ‘yan sanda amma abin ya cutura, sai dai wani jami’in dan sanda wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da faruwar hakan.

A cewar jami’in dan sandan ya ce, “Ofishinmu sun sami labarin wannan gidan kason na bogi inda ba mu yi jinkiri ba, muka ziyarci wannan wajen”.