Burkina Faso da Mali da Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soja, sun kammala shirye-shiryen samar da ƙungiyar gamayyar ƙasashen.
Lamarin na zuwa ne bayan da ƙasashen suka juya wa Faransa da ta yi musu mulkin mallaka baya, inda suka karkata akalarsu wajen Rasha a yanzu.
- Yadda matan Kannywood suke ƙarkon kifi a kan maza
- Ta’addancin ’yan bindiga ya ragu da kashi 70 a Katsina — Dikko Radda
Ministocin harkokin wajen kasashen sun gudanar da wata ganawa a ranar Juma’a a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, domin cimma yarjejeniyar kafa kungiyar hadin kan kasashen Sahel wato AES.
A cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare ya fitar, ya ce shugabannin ƙasashen uku ne za su sanya hannu kan yarjejeniyar da suka cimma, duk da dai bai bayyana ranar da za a yi hakan ba.
A watan Janairun wannan shekarar ce ƙasashen uku suka sanar da ficewarsu daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta a Yamma ECOWAS wacce suka zarga da zama ‘yar amshin shatan Faransa, don haka suka samar da ta su ƙungiyar.
Dangantaka tsakanin ƙungiyar ECOWAS da ƙasashen uku ta yi tsami bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a watan Yuli da Burkina Faso a shekarar 2022 da kuma Mali a shekarar 2020.
ECOWAS dai ta yi kira ga dukkan ƙasashen uku da su koma kan tsarin mulkin farar hula.
A ƙoƙarin da take yi na yi wa tufkar hanci, tuni ƙungiyar ta ECOWAS ta ɗage kusan dukkan takunkuman da ta kakaba wa ƙasashen uku.
Yankin Sahel dai na fama da matsalolin tsaro na ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, dalilin da ake ganin ya haifar da juyin mulki a ƙasashen.