✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto matashiyar da aka yi garkuwa da ita

An cafke mutum daya da ake zargin na da hannu wajen garkuwa da ita

’Yan sanda a Jihar Binuwai sun tseratar da wata matashiya daga hannun wadanda suka yi garkuwa da ita.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu bata-gari suka yi garkuwa da matashiyar a lokacin bikin Easter, a ranar Lahadi a gidansu da ke Karamar Kukumar Kwande a jihar.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa yarinyar mai suna Mngusuur Iorlian, an sace ta tare da yin garkuwa da ita ne da misalin karfe 12 na rana.

Sai dai binciken ’yan sanda ya ba su nasarar cafko wani mutum da ake zargin yana da hannu wajen sace matashiyar.

Mazaunin yankin ya shaida mana cewar matashiyar ta kubuta sannan an mika ta ga iyayenta.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta ce bayan kubutar da yarinyar tare da cafke mutum daya, rundunarsu ta tsaurara matakan tsaro don gano maboyar ragowar masu garkuwa da matashiyar.