✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto hadimin Gwamnan Kuros Ribas da aka sace

An ceto Mista Ofuka awanni kadan bayan yin garkuwa da shi a ranar Talata.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Ribas, ta tabbatar da ceto Hadimin Gwamnan Jihar Kuros Riba, Mista Oscar Ofuka daga hannun wanda suka yi garkuwa da shi a ranar Talata.

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar, Kayode Sikiru Akande ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar salula da wakilin Aminiya.

  1. An kama ’yan Boko Haram biyu da maganin karfin maza a Borno
  2. Ta yanke mazakutar mijinta ta soya

Sai dai jim kadan da sace shin, ya ce tuni ’yan sanda suka sami nasarar ceto shi.

A cewarsa, hadimin ya shaki iskar ’yanci ne bayan jami’ansu da suka baza sun sami nasarar ceto shi.

Kwamishinan ya ce, “Mun sami nasarar ceto shi ’yan sa’o’i da sace shi.

“Ku ’yan jarida kun jima kuna zarginmu, yanzu kuma mun yi abin fada, ya kamata a yaba mana,” inji shi.

Sai dai wasu majiyoyi sun ce wasu jami’an ’yan sanda da ake zargin daga shalkwatarsu ta Abuja aka turo su ne suka dauke hadimin bayan an yi korafi a kanshi.