Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke ’yan daba 61 a wajen taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya sanar da hakan a ranar Alhamis.
- Masarautar Bauchi ta nada sabon Waziri
- Gwamnatin soja ta fi ta farar hula tausayin malaman jami’a – ASUU
“Mun kwato wukake 33, lauje takwas, tabar wiwi, kwaya da sauran kayan maye a hannunsu,” in ji shi.
Kiyawa ya ce hakan na daga cikin shirin rundunar na ganin an yi zaben da ke tafe lafiya, tare da kawo karshen ayyukan ’yan daba a jihar.
Ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike a kansu za ta mika su kotu don yanke musu da hukunci.
A baya-bayan nan dai ayyukan ’yan daba sun kara kamari a Jihar Kano bayan fara yakin neman zaben ’yan siyasa.
A ranar Laraba ne dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da yakin neman zabensa a jihar.
Sai dai an yi zargin cewar ’yan daba sun ci karensu ba babbaka.