✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke wanda ya kashe dalibar Jami’ar Jos

An tsinci gawar dalibar a dakin otal an cire wasu sassan jikinta.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta cafke wani matashi da ake zargi da kisan wata dalibar Jami’ar Jos, Jennifer Anthony, wadda aka tsinci gawarta a wani dakin otal a Jos.

Aminiya ta rawaito yadda aka tsinci gawarta dalibar a cikin wani dakin otal an cire wasu sassa na jikinta.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Bartholomew Onyeka, yayin gabatar da wanda ake zargin tare da gungun wasu ’yan fashi 27 da aka kama tare a ranar Talata, ya ce ana ci gaba da bincike.

Kwamishinan ya ce wanda ake zargi da kisan dalibar saurayinta ne wanda tun bayan samun gawarta aka nema shi aka rasa.

Ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike za ta mika shi a gaban kotu don yanke masa hukunci.

Har wa yau, Kwamishinan ya roki jama’a da su kasance masu taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimakawa wajen yaki da bata-gari a jihar.

Tuni rundunar ’yan sandan ta mika gawar dalibar ga dakin bincike na musamman don gano hakikanin abin da ya yi sanadin mutuwarta.