Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwai, ta ce ta kama mutum shida da laifuka daban-daban na zabe a zaben shugaban kasa da na ’yan majalisun tarayya da aka kammala a jihar.
Kakakin rundunar, SP Catherine Anene ce, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Makurdi.
- DSS ce abokiyar hamayarmu a Kano ba APC ba —NNPP
- Zaben Gwamnoni: A guji siyasar ko a mutu, ko a yi rai —Jonathan
Kwamishanan ’yan sandan Jihar Benuwe, CP Wale Abass, ya yaba wa jami’an da suka kama masu laifin a lokacin zaben.
Ya bayyana cewa mutum shidan, ana ake zargin su da laifin mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, da kwace akwatunan zabe da kuma mallakar katin zabe guda tara ba bisa ka’ida ba.
“A cewar CP, an kammala bincike, an kuma aike da takarda ga hukumar zabe, domin ci gaba da daukar matakin da ya dace.
“Ama kuma gargadin masu laifin zabe da su guji irin wannan rashin bin doka da oda domin hukuma ba za ta raga musu ba,” in ji ta.
Ta kara da cewa kwamishinan ’yan sandan jihar, ya umarci kwamandojin ’yan sanda na sassan jihar da su tabbatar an gudanar da zabukan cikin lumana a yankunansu a ranar Asabar.