✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke mata da miji da kan mutum a Ogun

Rundunar ’Yan sandan jihar Ogun ta kama miji da mata da bokansu bisa laifin yanko kan wani mamaci bayan sun tono kabarinsa. Mai magana da…

Rundunar ’Yan sandan jihar Ogun ta kama miji da mata da bokansu bisa laifin yanko kan wani mamaci bayan sun tono kabarinsa.

Mai magana da yawun Rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, an kama ma’auratan  Niyi da Remilekun Folorunso, da Muyideen Tolubi da wani boka, Sonubi Taiwo, bayan sun yanko kan daga gawar wani mamaci.

Oyeyemi ya ce, an kama su ne ranar Alhamis tare da taimakon wanda ya sanar da rundunar cewa ya gansu suna tono gawar mamacin a Odogbolu, amma kafin a isa wurin sun tsere bayan sun cire kan mamacin.

Ya ce, sakamakon haka ne DPO na Odogbolu, CSP Afolabi Yusuf, ya baza komarsa kuma aka yi nasarar kama wadanda ake zargin.

“Sun kuma tabbatar wa ’Yan sanda cewar su suka tone kabarin suka sare kan mamacin.”

“Daga baya suka kai masu bincike har wajen bokon da ya sa su kai masa kan mutum don a yi musu tsafi.”

Oyeyemi ya ce Kwamishinan ’Yan sanda, Edward Ajogun, ya bayar da umurnin a mayar da wadanda ake zargin zuwa sashen bincike da gurfanar da wadanda suka aikata manyan laifuka.