Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta cafke wasu mutane da suka kware wajen safarar miyagun kwayoyi da sauran kayan maye a kananan hukumomi biyu a jihar.
Wannan ci gaban na zuwa ne sa’o’i 24 bayan kama wani fitaccen mai safarar miyagun kwayoyi a Karamar Hukumar Auyo ta jihar.
- Zan karasa aikin da Buhari ya fara na cefanar da NNPC — Atiku
- Kasuwar masana’antar Nollywood ta yi faduwa mafi muni a tarihinta
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shisu Adam, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce an kama mutanen ne a samame da suka kai a kasuwannin da lamarin ya shafa.
Ya ce yanzu haka ana bincike a kan laifin da ake zarginsu da aikatawa.
Rahotanni sun ce an kama wadanda ake zargin ne a tsakanin ranar Litinin zuwa Talata a kananan hukumomin Guri da Kirikasamma na jihar.
Kakakin ’yan sandan jihar, ya bayyana cewa, a lokacin da ’yan sandan suka kai samame a kasuwar Kirikasamma, sun gano kullin tabar wiwi guda 95 a cikin leda da kwayar Tramadol da kuma almakashi guda biyu.
Ya ce, “A ranar 18 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 7:30, bisa sahihin bayani, wata tawagar ’yan sanda ta kai samame a kauyen Marma, Karamar Hukumar Kirakasamma.
“An kama wasu mutum biyu da ake zargi, wadanda dukkansu mazauna kauyen Marma ne.”
A samamen da aka kai Guri kuma, ya ce DPO, CSP Adamu M Danjuma, ya jagoranci kama wani mai shekara 34, a garin Guri, yayin da wasu suka tsere.
An samu tabar wiwi guda 100 a tare da shi da kuma nau’in kayan maye ire daban-daban.
Ya ce za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu domin, kuliya manta sabo ya zartar musu da hukunci.