Jami’an ’yan sanda a garin Ilorin, Jihar Kwara sun cafke malamin da ya cika wandonsa da iska, bayan jefa dalibinsa doguwar suma.
An cafke malamin ne bayan shigar da kara a kansa a caji ofis din yankin Oloje, bisa zargin yi wa dalibin bulala 6,000.
- Almajiran Abduljabbar na roko a bude masallacinsa
- Harin Imo: An girke jami’an tsaro don kare Hausawa
- Ramadan: Hanyar magance sabanin ganin wata —Farfesa Mansur
- Yajin aiki: Gwamnati za ta tattauna da likitoci
A ranar Alhamis, Aminiya ta kawo rahoton yadda malamin ya yi wa almajirin dukan wuce kima saboda zargin sata.
Kafin yi wa yaron bulalar, sai da malamin ya sa karti biyar suka tale shi a kan tebur, sannan ya shiga zabga masa dorina, kuma bai tsahirta ba sai da aka yi wa yaron bulala 6,000 a matsayin haddi.
Rahotanni sun bayyana cewa za a mayar da lamarin sashen kula da laifukan jinsi na Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Kwara.
Tun bayan da malamin ya samu labarin an shiga da karar sa gaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta jihar, nan take ya ranta a na kare.
An ruwaito cewar, dalibin an kwantar da shi a asibitin Mimtaz da ke yankin Apalara, a karamar hukumar Ilorin ta Yamma a jihar.