✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke bata-gari 87 a Borno

Tuni aka gurfanar da wasu daga cikinsu a gaban kotu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta cafke wasu bata-gari 87 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban ciki har da masu kai wa Boko Haram bayanai.

Sauran mutanen da rundunar ta cafke sun hada da wadanda ake zargi ’yan fashi ne da barayi da masu aikata fyade da ’yan sara-suka da dai sauransu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar,  Abdu Umar, ya tabbatar da hakan yayin gabatar da wadanda ake zargin a ranar Talata a hedikwatar ’yan sandan da ke birnin Maiduguri.

Ya ce an gurfanar da mutum 67 daga cikinsu a gaban kotu tare da tisa keyarsu zuwa gidan gyaran hali.

“A ranar 29 ga watan Afrilum 2022, hukumar leken asiri ta ’yan sanda ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da alaka da Boko Haram da kuma kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP,” inji shi.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya bayyana yadda aka cafke wasu da suka yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyade.

Ya ce, “A ranar 30 ga watan Mayun 2022, bayan samun rahoton da ’yan sanda suka yi a sansanin makiyaya da ke unguwar Njimtilo da ke Maiduguri, sun kama wasu mutum shida da ake zargi da alaka da kungiyoyin masu garkuwa da mutane daban-daban da suka addabi yankin Mubi da ke Kudancin Jihar Borno da Jihohin Adamawa da Taraba.

“Kazalika, an kama wani da ake zargi da laifin satar shanu a yankin Njimtilo,” kamar yadda Kwamishinan ya bayyana.