Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum biyar da ake zargin barayin shanu ne, inda ta kwato shanu hudu a jihar.
Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ne, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a garin Tafa da ke Karamar Hukumar Kagarko.
“A ranar 30 ga watan Disamba, 2023, jami’anmu sun samu sahihan bayanai, inda suka kama wani da ake zargi mai shekara 20, suka kawo shi caji ofis,” in ji shi.
Ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ranar Litinin cewa wanda ake zargin yana da wasu shanu hudu da ake zargin na sata ne.
Ya bayyana cewa bayan bincike, ogan wanda ake zargin ya amsa cewa shugaban wata gona da ke garin Sabon Wuse ne ya ba shi amanar kiwon shanun.
“Babban wanda ake zargin ya ce sun hada baki ne da sauran mutum hudun sun sayar da shanun da suka sace,” in ji shi.
Hassan, ya ce wadanda ake zargin dukkansu suna hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.