’Yan sanda a Jihar Gombe sun kama wani matashi daga garin Bandila da ke Karamar Hukumar Gulani ta Jihar Yobe ya saci shanu 21.
Da yake gabatar da wanda ake zargin a ofishin ’yan sanda na garin Bajoga, kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a ranar 6 ga watan Yuni ne wani dattijo mai shekara 75, Jauro Ahamdu, da ke garin Shuwari a yankin Bajoga ya kai rahoto ofishin cewa an sace masa shanu 21 cikin dare, wanda kudinsu ya kai Naira miliyan bakwai.
Bayan nan ne DPOn Bajoga ya tura jami’ansa suka shiga bincike inda suka kama wanda ake zargin yana kokarin ketara Kogin dake iyakar Jihar Gombe da Yobe, kuma nan take ya amsa laifinsa.
Ya ce an samu duka shanun guda 21 da duk wasu kayayyaki da ake zargin sacewa tare shanun a wurinsa.
- Wa zai fi samun kudi: Tsakanin Messi a Inter Miami da Ronaldo a Al-Nassr
- Buhari ya kashe wa matattun matatu fiye da kudin gina Matatar Dangote —Gwamnan Nasarawa
Da wakilin mu yake tambayarsa dalilin sace shanun, sai ya ce yana tafiya ne cikin dare kawai sai ya yi karo fa shanun a garkensu, shi kuma kawai sai ya kada su ya tafi da su.
Ya ce yana tafiya da shanun zai koma garin sua Jihar Yobe sai ’yan ssanda da maharba suka kama shi suka juyo da shanun.
A cewarsa, bai taba satar shanu ba, su din ma da ya sata zai dinga kiwata su ne yana sayarwa yana biyan bukatarsa.
Yanzu dai yana hannun ’yan sanda kuma sun ce da zarar sun kammala bincikensu za su tura shi zuwa kotu.