✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke 3 daga cikin masu zanga-zanga kan batanci ga Annabi a Maiduguri

An kama su ne yayin zanga-zangar batancin da wata a yi wa Annabi (S.A.W) a Maiduguri

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da kama mutum uku yayin zanga-zanga a Maiduguri don nuna rashin jin dadin batancin da wata mai suna Naomi Goni ta yi wa Annabi Muhammad (SAW) a shafinta na Facebook.

An zargi Naomi da yin batancin ne yayin da take martani a kan kisan da aka yi wa dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, Deborah Samuel, sakamakon batancin da ta yi a kan Fiyayyen Halitta.

Sa’ilin da yake yi wa manema labarai jawabi a hedkwatar rundunar da ke Maiduguri a ranar Litinin, Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Abdu Umar ya ce sun kama mutum ukun ne dauke da wani abu a cikin jarka mai kama da fetur.

Daga nan, Kwamishinan ya gargadi mazauna yankin da kada su yi amfani da damar zanga-zangar wajen ta da zaune tsaye a Jihar.

Ya ce, “Ana tsare da wadanda aka kama din, amma ba na tunanin sun aikata wani laifi sai bayan kammala bincike za mu tabbatar da hakan.”

Jami’in ya kara da cewa, an haramta duk wani taro ba bisa ka’aida ba a fadin Jihar, tare da cewa jami’ansu na ci gaba da sintiri domin tarwatsa duk wani haramtaccen taro da aka shirya.

Daruwan mutane ne suka yi dandazo a kusa da barikin sojoji na shiyyar ta bakwai, wato Garrison da ke birnin Maiduguri ranar Litinin, inda a nan aka ce Naomi ke da zama don yin zanga-zangar nuna rashin jin dadin batancin da ta yi.

Masu zanga-zangar sun kona tayoyi da kuma kashe babbar hanyar da ke yankin.

Sai dai duk kokarin da aka yi domin jin ta bakin kwamandan barikin ya ci tura.