’Yan sanda sun bude wa masu zanga-zangar #EndSARS wuta tare da kashe biyar daga cikinsu a unguwar Dutsen Alhaji, da ke yankin Bwari, Abuja.
Rahotanni sun ce hakan ta sa masu zanga-zangar banka wa ofishin ’yan sandan da ke unguwar wuta tare da kona motoci da dama da ke ajiye.
- ’Yan daba sun kashe mutum uku a zanga-zangar #EndSARS
- ’Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar #EndSARS a Kano
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa da misalnin karfe 8 aka fara zanga-zangar cikin lumana “kafin isowar motoci hudu na ‘yan sanda da suka fara harbe-harben da ya yi sanadiyyar mutuwar biyar daga cimin masu zanga-zangar.
“Hakan ya fusata sauran matasan suka je suka cinna wa karamin ofishin ‘yan sandan da ke yankin wuta tare da kona wasu motoci”.
Shaidan ya ce faruwar hakan ke da wuya sai ‘yan sandan suka bar wurin yayin da aka wuce da gawarwakin masu zanga-zangar da suka mutu zuwa Babban Asibitin Bwari.
Wakilinmu ya nemin jin ta bakin ‘yan sanda, amma suka ce za su tuntube shi daga baya.
Karin labarin na tafe….