Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta tabbatar da kashe ’yan bindigar da suka kashe tsohon hadimin shugaban kasa, Ahmed Gulak.
Wannan na dauke cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, SP Bala Elkana ya fitar a ranar Lahadi.
- Kisan Gulak: Kungiyar matasa ta yi barazanar daukar mataki
- Likitoci sun tsawaita lokacin shiga yajin aiki da mako biyu
Ya ce, “Bayan samun rahoton kashe Ahmed Gulak da ’yan bindiga suka yi, an hada rundunar fikira ta musamman wadda aka tura zuwa wurin da abin ya faru a Mahadar Obiangwu a Karamar Hukumar Ngorokpala a Jihar Imo.
“Rundunar ta yi nasarar gano wasu bayanai game da wadanda suka kashe Gulak.
“Direban da ya dauki Gulak zuwa filin jirgi ya ba da cikakken bayani game da wadanda suka aikata kisan da irin motar da suka hau.
“Bayanan sun bayyana maharan sun yi amfani da mota kirar Toyota Camry 2005, Toyota Sienna 1998, Toyota fara kirar Hilux da kuma Lexus RX 330.
“Lambobin motar an boye su saboda wasu dalilan tsaro
“Bayan samun bayanan maharan da kuma irin motocin da suka yi amfani wajen kashe Gulak, ba mu bata lokaci wajen bin sahunsu ba.
“Cikin kankanin lokaci muka gano inda suka shiga, nan take aka musu kawanya a yankin Afor Enyiogugu na Karamar Hukumar Aboh-Mbaise.
“Ko da suka hangi jami’an ’yan sanda, sai suka fara harbe-harbe, mu ma nan take mu ka bude musu wuta, muka kashe shida daga cikinsu, hudu kuma suka ji munanan raunuka, motocin da suka kai harin da su kuma duk an yi nasarar kwato su.”
Elkana ya kara da cewa an samu bindigogi da sauran makamai daga hannun maharan.
“An samu kunshin harsasai na AK-47 guda uku, karamar bindiga guda daya, bindigogi kirar AK-47 guda biyar da sauran makamai.
“An gano wadanda suka kai harin mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB ne da kuma reshenta na ESN.
“Direban da ya tuka Gulak kafin rasuwarsa da sauran mutanen da ke cikin motar, duk sun shaida fuskokin wadanda aka kashe a matsayin wadanda suka kashe Gulak,” cewar Elkana.
Tuni aka yi wa Ahmed Gulak jana’iza tare da binne shi a makabartar Gudu da ke Abuja a ranar Lahadi.