✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ƙwato shanun sata a hannun Lakurawa

’Yan sanda sun ƙwato shanun da ’yan ta’addan Lakurawa suka sace a ƙauyen Nastini da ke Jihar Kebbi

’Yan sanda a Jihar Kebbi sun yi nasarar ƙwato wasu daga cikin shanu 200 da mayaƙan Lakurawa suka yi fashin su a ƙauyen Nastini.

A yayin harin ne ’yan ta’addan suka kashe ’yan sanda biyu tare da yin aown gaba da dabbobin a ranar Alhamis.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar ya bayyana cewa an kai harin ne a wata gidan da ke kusa sa wata rugar Fulani a ƙauyen Natsini da ke kan hanyar Argungu zuwa Kangiwa.

Bayan samun labarin harin ne ’yan sanda suka kai ɗauki inda aka yi fatattaki ’yan ta’addan.

Ya ce ’yan ta’addan sun tsere da raunukan harbi, amma an yi rashin sa’a ’yan sanda biyu sun kwanta dama a yayin musayar wuta.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M. Sani da Sarkin Argungu, Alhaji Dakta Sama’ila Muhammad Mera sun ziyarci yankin domin gane wa idansu da kuma jajanta wa iyalan mamatan.