✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda na tsare da Kofur Barau da ya yi wa yarinya fyade

A garin Anacha, Jihar Anambara kuwa, ’yan sanda sun tabbatar da cewa suna tsare da Kofur Barau Garba, wanda ake zargi da boye wata yarinya…

A garin Anacha, Jihar Anambara kuwa, ’yan sanda sun tabbatar da cewa suna tsare da Kofur Barau Garba, wanda ake zargi da boye wata yarinya ’yar shekara 14 na tsawon kwana shida, inda shi ma ya yi mata fyade har ta samu raunuka a matuncinta.

A makon jiya ne dai aka samu korafi kan zargin da aka yi wa Kofur din, cewa ya killace yarinyar a unguwar Okpoko kuma ya yi mata fyade fiye da kirga, har tsawon kwana shida. An samu tabbacin cewa an tura shi aiki na musamman ne daga Sakkwato zuwa Anambra. 

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Anambra Umar Garba ya bayyana cewa a yanzu haka suna kan yi masa tuhumar cikin gida kamar yadda ka’idar aikin ’yan sanda ta tanada. Kamar kuma yadda ya ce, da zarar sun kammala sauran bincike, za su gurfanar da shi a gaban kotu.

Ya kara da cewa jami’in da ake zargi ya amsa tuhumar cewa ya killace yarinyar a dakinsa amma ya musanta zargin cewa ya yi mata fyade. “Ya zuwa yanzu, ba mu samu sakamakon binciken likita ba daga asibiti amma binciken da muke cikin yi zai tabbatar da shaidar ko an yi wa yarinyar fyade ko akasin haka,” inji shi.

Ya bayyana cewa wannan laifi babba ne da ya saba wa ka’idojin aikin ’yan sanda a Najeriya, don haka za su yi dukkan abin da ya dace domin ganin an yi adalci a cikin al’amarin. “Hukuma za ta tabbatar da cewa an samar da adalci kan al’amarin. Duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci komai matsayinsa,” a cewar kwamishina.