Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara na neman wasu mutum biyar ruwa a jallo bisa zargin kisan gilla da aka yi wa wani likita a garin Gusau.
’Yan bindiga sun kutsa gidan Dakta Enoch Okoara da ke a unguwar Mareri, a kwanakin baya, inda suka nemi ya ba su kudi amma ya ki, su kuma suka kashe shi ta hanyar sara da adda suka kuma cinna wa gawarsa wuta.
- Wadume: Kotu ta dage sauraron shari’ar ta’addanci
- ‘Mutum 23 ne ‘yan bindiga suka kashe a harin Zamfara’
- Za mu kwace lasisin duk likitan da ke watsi da marasa lafiya – Minista
“Muna neman sauran kuma za mu kama su don tabbatar ba su guje wa shari’a ba. Idan mun kama su kuma muka gama bincike za mu kai su kotu”, inji Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Usman Nagogo.
Kwamishin ‘yan sandan ya ce rundunar ta kama wani wanda ya tabbatar da cewa da hannunsa a kashe likitan.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan ’yan sanda sun lalata wani shirinsu na yin garkuwa da wani mutum, sai dai har yanzu akwai wasu wadanda rundunar take nema ruwa a jallo.
Da ake gabatar da shi ga ‘yan jarida, wanda ake zargin ya ce wa ya kashe mutum akalla bakwai a hare-haren da suka kai a kan wani kauye a karamar hukumar Kaura Namoda.