✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

’Yan Sanda na binciken dalilin mutuwar matasa 21 a gidan giya a Afirka ta Kudu

’Yan Sanda na binciken wani gidan giya don gano musabbabin mutuwar wasu matasa 21 da suka je holewa da dare a kasar Afirka ta Kudu.…

’Yan Sanda na binciken wani gidan giya don gano musabbabin mutuwar wasu matasa 21 da suka je holewa da dare a kasar Afirka ta Kudu.

Matasan da yawancinsu ba su dara shekaru 13 ba, an gano gawarsu a mashayar da ke birnin East London a Kudancin kasar, yayin da wasu suka ce ga garinku nan bayan kai su asibiti.

’Yan sandan sun ce ba a samu wani rauni a jikin matasan ba, abin da ya sanya suke zargin matsalar daga giyar da suka sha ne, kasancewar ba su kai shekarun shan ta ba.

Kakakin Sashen Lafiya ta lardin, Yenola Dekede, ta sanar da kamfanin dillancin Labarai na AFP cewa suna binciken ko guba aka sanya musu a giyar, ta yi sandiyar mutuwarsu.

Ta ce sun fara binciken ne tun a daren Talata, kuma da zarar ya kammala washegari Laraba za su sada gawarwakin da iyalansu.

Wadanda wannan mummnan lamari ya ritsa da su dai yawancinsu dalibai ne da suka je mashayar domin murnar kammala karatun sakandare, kamar yadda kakakin ’yan sandan yankin Thembinkosi Kinan ya bayyana.

Tuni dai tawagar jami’an bincike na musamman daga babban birnin kasar, Pretoria ta isa yankin  domin ci gaba da bincike

Kasar Afirka ta Kudu ta haramta shan giya ga wadanda shekarunsu ba su kai 18 ba, to sai dai bayanai na nuna gidajen giyar da ke birane galibi  ba su cika bin wannan doka ba.