✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Sanda Mata Sun Tallafa Wa Marayu 300 A Gombe

Wasu ’yan sanda mata a Jihar Gombe sun yi karo-karo kudade suka sayi kayan abinci suka kai gidan marayu na Musulmi da na Kirista a…

Wasu ’yan sanda mata a Jihar Gombe sun yi karo-karo kudade suka sayi kayan abinci suka kai gidan marayu na Musulmi da na Kirista a unguwar Tumfure da ke fadar jihar.

’Yan sandan a karkashin jagorancin ASP Esther Musa, sun kai wa gidaje marayun buhunan masara da kwalayen sabulun wanka da omo da takalma da tsabar kudi.

Da take jawabi a gidan marayu na Kirista mai suna Christian Covenant & Orphans Foundation ASP Esther Musa, ta ce kungiyarsu mai suna Strong Binding ce ta ga ya dace su tara dan wani abu a tsakaninsu su tuna da marayu.

Ta ce sun taimaka ne da dan abin da ya sauwaka domin ya fi ace ba su yi ba amma da son samu ne da abin da suka bayar din yafi haka.

Da ya ke marabta su Daraktan gidauniyar ta Christian Covenant & Orphans Foundation Mista EL-Polycarp Y Degri, ya ce sun ji dadi bisa wannan dauki da ’yan sanda mata suka kawo musu domin da kowa zai dinga tunawa da yara  marayu a irin wadannan gidajen da za a samu saukin kula da su.

El-Polycarp, ya ce hatta tallafin abinci da gwamnati take bayarwa ba a taba ba su ba, irin wadannan mata ’yan sanda da kungiyoyi ne suke kokari a kan su.

Ya ce gidan marayu na tumfure reshe ne nasu domin babban gidan yana garin Degri a karamar hukumar Balanga inda suke da marayu 260 kuma duk tallafin da aka ba su suna rabawa gidajen ne kowa su samu.

A gidan marayu na Musulmai, sun ba da irin wannan tallafi inda shugaban gidan  Dokta Babayo Kolo, ya nuna jin dadinsa matuka, musamman ganin cewa gwamnati ba ta taba ba su wani kudi ko kayan abinci na don kula da marayu ba,  amma daidaikun jama’a da kungiyoyi sune masu kai musu tallafi.

Dokta Babayo Kolo, ya yi kira ga gwamanti da masu hannu da shuni da su yi koyi da ’yan sanlnda mata da suka kai musu wannan tallafi, ko da yake hakan ba abun mamaki bane domin mata sun fi tausayi wajen kula da yara.

Ya ce a halin yanzu suna da marayu 60 ne, sauran sun girma an aurar da su, mazan kuma sun balaga an yaye su.

ASP Esther Musa, ta ce da suka zo su ka bada kayan zuciyar su ta kadu matuka inda tace a shekara mai zuwa za su duba yiwuwar kara yawan abin da za su bayar.