✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun harbe dan Najeriya a Ghana

Wasu matasa sun yi cincirindo a canji ofis din ‘yan sandan yankin Gomoa Buduburam da ke kasar Ghana bayan wani dan sanda da harbe wani…

Wasu matasa sun yi cincirindo a canji ofis din ‘yan sandan yankin Gomoa Buduburam da ke kasar Ghana bayan wani dan sanda da harbe wani dan Najeriya.

Matasan wadanda akasarinsu ‘yan Najeriya ne sun yi wa ofishin ‘yan sandan kwanya a ranar Asabar, 18 ga watan Julin 2020.

Kwamandan ‘yan sandan lardin Kasoa, ya tababtar da faruwar lamarin a zantawarsa da wani gidan radiyo a Accra babban birnin kasar.

Ya ce dan Najeriyan mai suna Walter Billions wanda ya yi tatul da giya, ya yi barazanar illata ‘yan sandan da aka kira su kwantar da tarzoma a ranar Juma’a, 17 ga watan.

Wani shugaban ‘Yan Najeriya mazauna Gomoa Buduburam, Emmanuel Chukuamaka Azubuike ya ce dan Najeriya da aka harbe ba ya cikin hayyacinsa a lokacin, don haka babu dalilin harbin sa.

Ya ce sun kai maganar ga rundunar ‘yan sandan lardin domin su gudanar da bincike.

“Na sanar da ofishin jakadancin Najeriya a Ghana halin da ake ciki, sun kuma ba ni umarnin bin ka’idojin doka, wato na kai maganar ga ‘yan sanda domin su fara bincike.

“Kwamandan ‘yan sandan ya shaida min cewa za a hukunta duk wani mai hannu a lamarin, yanzu haka matasanmu sun hassala, da mutumin da ‘yan sanda suka kashe yana da niyyar cutar da wani ai da ya yi hakan kafin su kai ga kashe shi.

“Yanzu muna jira mu ga matakin da za su dauka”, inji shi.

A baya-bayan nan ma an samu takun saka a tsakanin kasashin biyu bayan wasu ‘yan Ghana sun rushe wani gini mallakar ofishin jakadancin Najeriya a kasarsu.

Daga bisani aka sasanta tsakanin kawayen biyu da duniya ke kallo a matsayin manyan kasashen Afirka masu kyakkyawar dangantaka.