✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe ’yan sanda 229 a Nijeriya —Bincike

A shekarar 2023 kadai an yi wa ’yan sanda 118 kisan gilla, wasu 111 kuma aka kashe su a watanni 10 na farkon shekarar 2024…

Binciken Aminiya ya gano yadda aka yi wa ’yan sanda 229 kisan gilla a bakin aikinsu a cikin watanni 22 daga suka gabata a fadin Nijeriya.

’Yan sandan da suka kwanta dama sun gamu da ajalinsu ne daga watan Janairun shekarar 2023 zuwa Oktoban 2024, amma duk da haka sun bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa wajen gudanar da aikinsu na kare rayuka da dukiyar al’umma ba.

A shekarar 2023 kadai, an kashe ’yan sanda 118 a masu mukamai daban-daban, sai wasu 111 da suka aka halaka a wani 10 na farkon shekarar 2024 da muke ciki.

Sun gamu da ajalinsu ne a hannun ’yan ta’adda da suka hada da ’yan bindiga da mayakan Boko Haram da ’yan kungiyoyin asiri da ’yan fashi da makami.

Na baya-bayan nan shi ke kisan wani dan sanda mai mukamin ASP, Augusine Osupayi, wanda aka yi wa kisan gidalla a lokacin da yake kokarin hana jama’a daukar doka a hannunsu a yankin Agege da ke Jihar Legas.

Munin lamarin a 2023

Akalla ’yan sanda 12 ne aka yi wa kisan gilla a watan Janairun 2023, sai wasu bakwai a watan Fabrairu, a jihohin Nasarawa da Neja da Binuwai da Imo da Anambra da Ebonyi da Delta.

A watan Maris an kashe wasu 11, lamarin da ya kara muni zuwa 23 a Afrilu, ciki har da wasu shida da ’yan fashin daji suka yi wa kisan gilla a Jihar Kebbi ranar 30 ga wata, wasu biyar kuma ’yan bindiga suka kashe su ranar 21 ga watan a Jihar Imo.

A cikin watan Mayu 17 sun kwanta dama, sannan a Yuni aka yi wa wasu ’yan sanda 31 kisan gilla.

Daga watan Agusta zuwa Dismbar 2023 kuma, ’yan sanda 22 ne suka gamu da ajalinsu a Jihar Binuwai.

Hare-haren 2024

A farkon shekarar 2024 da muke ciki kuma bata-garin sun hakala ’yan sanda 15, ciki har da wasu bakwai a Jihar Delta.

A watan Fabrairu mayakan kungiyar ta’addan Biafra (IPOB) suka yi wa ’yan sanda kisan gilla,  inda a Maris kuma, zauna-gari-banza suka kashe wasu 10 a jihohin Imo da Ebonyi da Anambra da Edo.

Ko gezau — in ji ’yan sanda

Wasu ’yan sanda da wakilinmu ya yi magana da su kan lamarin jajanta wa iyalan abokan aikin nasu da suka kwanta dama, amma sun ce hakan ba zai sa su kasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikinsu na kare al’umma kasa.

Daga cikinsu akwai wanda ya ce, “hakika abin takaici ne yadda bata-gari suka yi wa abokan aikinmu kisan gilla, amma dukkanmu da ke wannan aiki mun san hadarin da ke cikinsa.

“Kowane aiki na da irin nasa hadarin, ana ganin namu ne saboda yawanci shi a bayyane yake. Amma gaskiyar magana ita ce, ko ba a kashe ka ba, a karshe dai dole sai ya mutu.”

Wani abokin aikinsa mai suna Abdul, ya ce, “Duk wanda ya rasu a wurin kare kasarsa, ya rasu a matsayin gwarzo. Saboda haka babu wani sabon abu, kuma abin da ya faru ba zai sa mu daina aikin da muke yi ba.”

Shi ma Ndifrike, ya jaddada cewa rasuwar abokan aikinsu a bakin aiki ba za ta sa su karaya ba, yana mai kira ga hukumar ’yan sandan Nijeriya ta kokarta wajen kula da iyalan mamatan, musannan yayan da suka bari.

“Domin akasarinmu da kake gani, mun sadaukar da rayuwarmu ga wannan aiki na kare al’ummar Nijeriya, duk abin da zai faru,” in ji shi.

Kara inganta kayan aikin jami’anku

Wani masanin tsaro, Abdullahi Garba, ya shawarci shugaban ’yan sanda Kayode Egbetokun, ya inganta tsaron jami’an rundunar ta hanyar samar musu da kayan aiki na zamani domin kare lafiyarsu a bakin aikinsu na yaki da laifuka.

A cewarsa, yin hakan ya zama dole domin “yakar masu laifi irin ’yan bindiga da ’yan fashi da sauransu sai an yi kyakkyawan shiri.”

Shi ma wani masanin tsaro, Silas Daves, ya bukaci ’yan sanda da su rika hada kai a lokacin gudanar da aiki, yana mai zargin cewa, ana kai musu harin kwanton bauna ne, “saboda wasu abokan aikinsu na ke bayar da bayanan sirri kan motsinsu ga masu laifi. Don haka ya kamata a kawar da bata-garin cikinsu,” in ji shi.

Daves ya ci gaba da cewa akwai babbar bukatar bunkasa binciken kwakwaf a rundunar.