✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan san sun kama Ronaldinho a Paraguay

Rahotanni daga kasar Paraguay na nuna cewa jami’ai sun zama tsohon dan wasan Brazil da Barcelona Ronaldinho. An kama tsohon dan wasan ne bisa zarginsa…

Rahotanni daga kasar Paraguay na nuna cewa jami’ai sun zama tsohon dan wasan Brazil da Barcelona Ronaldinho.

An kama tsohon dan wasan ne bisa zarginsa da yin amfani da takardar izigin shiga kasa wato fasfo na karya.

Mai shakera 39 din, wanda ya lashe duk kofin da kowane dan wasa ke sha’awar lashewa, ciki har da Kofin Duniya da Gasar Zakarun Turai da sauransu, an tsare shi ne tare da dan uwansa Roberto.

Ronaldinsho ya je kasar ce domin wani taro da Kamfanin Casino ya gayyace shi.

Shi dai Ronaldinho, yanzu ba shi da fasfo na kasar Brazil, saboda wani laifi da ya yi a shekarar 2018, wanda hakan ya sa aka karbe masa fasfon nasa.

An kama shi ne a lokacin da laifin ginda wajen kiwon kifi ba tare da izini ba, wanda hakan ya sa aka ci shi tarar Dala miliyan 8.5 a watan Nuwanban 2018.

Da ya kasa biyan kudin, sai Babbar Kotun kasar ta yanke hukuncin hana tsohon dan wasan fita kasar ta hanyar karbe fasfo dinsa.

Hakan ya sa ake tunanin sai ya yi fasfon na kasar Paraguay, wanda ‘yan sanda suka kama shi a kai, wanda ake zargin na karya ne.