Wasu ’yan sama-jannati sun dawo duniyarmu bayan sun yi kwanaki ɗaiɗai har 371 suna shawagi a sararin samaniya wanda hakan ya sa suka zama mutane na farko a duniya da suka taba yin haka a tarihi.
Frank Rubio dan kasar Amurka an harba shi zuwa sararin samaniya domin aikin gwaje-gwaje da bincike a tashar kasa-da-kasa (ISS) da ke sararin samaniya.
- Yaushe za a fara samun mata masu bayar da umarni a Kannywood?
- An ceto wasu daliban Jami’ar Gusau da aka sace a Zamfara
An yi hakan ne a karkashin Hukumar NASA mai bincike kan sararin samaniya, tare da ’yan kasar Rasha biyu, Sergei Prokopyev da Dmitri Petelin a ranar 21 ga Satumban bara.
An shirya za su dawo duniya a ranar 28 ga watan Maris, 2023, amma hakan bai yiwu ba, saboda haɗari da kumbon da ya kai su ya yi a lokacin da suke shirin dawowa a dalilin taho-mu-gama da wani dutse a samaniya, a watan Disamban 2022.
An dawo da kumbon nan duniya aka gyara, sannan aka sake aikawa da shi Tashar ISS inda Frank da sauran abokan aikinsa suke, kuma suka shiga ya dawo da su duniyar a ranar 27 ga Satumban da ya gabata.
A cewar jaridar labaran kimiyya ta Live science, Rubio shi da sauran ’yan sama-jannati Sergey da Dmitri sun dawo lafiya.