Biyu daga cikin cikin matafiya Sakkwatawa hudu da suka kamu da cutar coronavirus a jihar Oyo sun tsere daga inda aka killace su.
A kwanakin baya ne jami’an tsaro suka kame matafiyan su 11 a kan iyakar Oyo da Osun wadanda aka zarga da laifin taka dokar hana tafiye-tafiye a jihohin kasa domin gujewa yada cutar coronavirus.
Daga bisani gwaman jihar Oyo Seyi Makinde ya sa aka yi masu gwajin cutar, kuma saka makon gwajin ya tabattar da mutum hudu na dauke da cutar.
Sarkin Hausawan Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, Sardaunan Yamma, ya ki karbar matafiya bakwai da basu kamu da cutar ba, bayan da gwamnan ya turo su fadar sa da zummar a kai su jihar su ta asali.
Matakin na sarkin Hausawan yazo ne a daidai lokacin da ake zargin biyu daga cikin matafiyan da suka kamu da cutar coronavirus sun tsere daga inda aka killace su.
Gwamnatin jihar Oyo ta saba alkawarin komar da matafiyan Sakkwatawa, bayan sun keta dokar hana shige da fita, matakin da ta bayyana zata a dauka a lokacin da ta tsare su.
- Hudu cikin matafiyan Sakkwato da aka tsare a Oyo na da Coronavirus
- Coronavirus: Oyo za ta mayar da tallafin shinkafa
Gwamnatin jihar ta mika mutanen ne ga Sardaunan Yamma Sarkin Hausawan Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, inda ta nemi ya koma dasu jihar su ta asali, a maimakon mika su ga Gwamnatin Jihar Sakkwato kamar yadda Gwamna Seyi Makinde ya fadi tun ranar da aka kama su.
Sai dai Sarkin Sasa ya ki karbar mutanen kamar yadda daya daga cikin Hakimansa Sarkin Dawakin Yamma Alhaji Kabiru Pandogari yayi wa Aminiya bayani.
Ya ce “muna sane da cewa Sarkin Sasa yana tare da Gwamnati shi ne ma dalilin aika wa da wadannan mutane zuwa fadar sa da Gwamnatin tayi.
“Amma duk da haka matakin da ya dauka na kin karbar mutanen ya yi daidai domin gwamnati ce take da hurumin killace su a kebabben wuri da basu magani wanda babu irin wannan wuri a fadar Sarkin Sasa” inji shi.
Tun farko dai a ranar da aka kama mutanen Gwamna Seyi Makinde ya bayar da umarnin killace su da yi masu gwajin cutar COVID-19 kafin a koma da su Sakkwato inda suka fito.
Kuma sakamakon binciken ya nuna hudu daga cikin mutanen sun harbu da cutar, hakan ya sa Gwamnatin daukar matakin mika ragowar mutanen bakwai ga fadar Sarkin Sasa.
A daidai wannan lokacin, biyu daga cikin mutane hudu da aka killace a cibiyar bincike ta Olodo suka sulale suka gudu ba tare da sanin inda suka dosa ba.
Sakataren Labaran Gwamna kuma dan kwamitin yaki da cutar kurona a Jihar Oyo, Taiwo Adisa ya tabbatar wa Aminiya cewa wadannan mutane hudu da aka gano suna dauke da cutar suna nan har yanzu ana basu magani a cibiyar binciken ta Olodo.
Taiwo Adisa bai yi karin bayani a kan sauran mutanen ba sai dai ya ce yana zaton sun koma garuruwan su.