✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sa kai za su fara jagorancin yaki da ’yan bindiga a Sakkwato – Tambuwal

Ya ce za su yi hakan ne saboda sun saba da dazukan.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce ’yan sa kai za su fara jagorantar sauran jami’an tsaro wajen yaki da ’yan bingidar da suka addabi Jihar.

Ya bayyana hakan ne lokacin da sarakunan gargajiya na Jihar suka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Sakkwato ranar Alhamis.

Sarakunan dai na karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ne, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.

Gwamnan ya ce za su yi hakan ne saboda ’yan sa kan sun saba da dazukan da ’yan bindigar ke amfani da su a matsayin maboya.

“Ba mu da ’yan sa kai a Sakkwato. Abin da muke kokarin yi a yanzu shi ne mu kafa kwakkwarar tawaga da hadin gwiwar Fadar Sarkin Musulmi wadanda za su jagoranci sauran jami’an tsaro wajen zuwa inda ’yan bindigar suka yi sansani a dazuka,” inji shi.

Tambuwal ya lura cewa babu yadda za a yi yaki da ’yan bindigar ya yi nasara ba tare da taimakon jama’a ba.

A cewar gwamnan, akwai bata-gari daga cikin jama’a da ke taimaka wa ’yan bindigar wadanda ya ce dole a zakulo su.

“Wadannan mutanen suna samun nasarar kai hari ne a yankunanmu saboda suna da masu basu bayanai daga cikinmu.

“Saboda haka ya zama wajibi mutane su dauki ragamar kai rahoton irin wadannan mutanen a cikinmu ga hukumomin jami’an tsaro.

“Sai bango ya tsage kadangare kan samu wurin shiga,” inji shi.

Wasu daga cikin sarakunan gargajiyar da suka kai ziyarar sun nuna takaicinsu kan yawan hare-haren da ake kai wa yankunansu.