✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan PDP da ke jihar Zamfara suna da matsala – Sani Gwamna

Ganin yadda jam’iyyu suke gudanar da yaki neman zabensu cikin mawuyacin hali da fargaba da yadda suke jajircewa don lashe zabe, ya sa wakilinmu a…

Ganin yadda jam’iyyu suke gudanar da yaki neman zabensu cikin mawuyacin hali da fargaba da yadda suke jajircewa don lashe zabe, ya sa wakilinmu a Gusau ya tattauna da Kakakin Jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara Alhaji Sani Gwamna Mayanci Jarman Maru don jin ta bakinsa kan halin da jam’iyyarsu ke ciki:

Aminiya: Jam’iyyun siyasa a Jihar Zamfara suna zargin juna da laifin lalata kayayyaki da kone-konen ofisoshi da motoci, a jam’iyyarku kun iya tantance asarar da kuka yi zuwa yanzu?
Sani Gwamna: To ka san yadda jam’iyyarmu take da tsari da biyayya, Gwamnan jiharmu Abdul’aziz Yari Abubakar da ita kanta jam’iyyar sun ce duk abin da aka lalata a rubuta wa jami’an tsaro, a gaya musu abin da aka lalata. Kuma mun yi tsaye mun ga cewa wadanda suka yi barnar nan kada a kuskura a lalata
musu kayayyakinsu, to har yanzu muna jiran sakamako adadin abubuwan da aka lalata ko me ya faru da su, don haka a halin da  ake ciki ba za mu iya cewa ga adadin abin da aka bata ba, amma dai mun san
wuraren da aka je kamar kauran Namoda da Zurmi da Maru da Bungudu, duk inda suka je babu wani wuri da ba su lalata gidaje da shuguna da sauransu ba, wanda mun san ba haka ake yin siyasa ba.
Aminiya: Ana zargin magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP suna karbar katin zabe wasu suna ba su Naira dubu, wane mataki kuke dauka a jam’iyyance don dakatar da wannan abu?
Sani Gwamna: Wannan wanda bai san ’yancin kansa ba ne za a yi wa haka, wanda ya san ’yancin kansa ba zai yiwu a ba shi Naira Dubu a amshi katinsa ba. Suna yi ne ga wadanda ba su san ’yancinsu ba, kuma duk inda muka je sai mun kira mutane mu gaya musu mun wayar masu da kai cewa duk wanda ya ce ka ba shi katinka ya ba ka Naira dubu ko kudi, to kada ka ba shi, don kona ta za su yi.
Aminiya: Wane shiri kuka yi don wayar da kan matasa su kauce wa tayar da hankali?
Sani Gwamna: To ka san an ce Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganewa, duk inda muka tafi babu inda Jam’iyyar PDP za ta ce mun lalata mata kayayyakinta, wannan yana daga cikin matakin da muka dauka. Kuma mun ba jami’an tsaro dama cewa duk wanda aka ga ya dauki makami a kama shi, a kwace makamin, idan akwai hukunci, a hukunta shi yadda ya dace, wannan shi ne abin da muke kai kuma shi ne abin da shugabanninmu suka aza mu a kansa.
Aminiya: Ko akwai wadanda aka kama a cikin wadanda ake zargi da lalata kayayyaki da kone-kone a halin yanzu?
Sani Gwamna: To, a iya saninmu akwai wadanda jami’an tsaro suka kama, amma ba mu san irin hukuncin da aka yi musu ba, iyakaci dai mun san an kama wasu, batun yana hannun jami’an tsaro suna bincike.
Aminiya: Jami’iyyarku ta APC da ta kafa Gwamna tana yawan fadin ta yi wa jama’a aiki, kuma saboda su ne kuke son a sake zabenku, to cikin ayyukan wane aiki ne kuke alfahari da shi?
Sani Gwamna: Alfaharinmu shi ne alkawarin da Gwamna ya yi a lokacin da muke yakin neman zabe a wancan lokaci kashi 99 cikin 100 ya cika su, wannan abin alfaharinmu ne shi ya sa muke da kwarin gwiwar shiga kowane lungu da sakon wannan jiha ta Zamfara, mu gudanar da yakin neman a sake zabensa, da ba mu cika ba da ba mu da karfin gwiwar sake dawowa mu ce a sake zabensa.
Aminiya: Sau da yawa a wasu wurare ana samun ’yan takara da suke amfani da kalamai masu harzuka mutane, wane mataki kuke dauka a banagrenku don kauce wa haka?
Sani Gwamna: Ai wannan ba sai ka yi magana ba, domin ko abokan adawa da suka yi abin ba a maida musu martani ba, yanzu shi ne suke son su sake dawowa a yi fitina, abin da muka dauka shi ne wannan jihar ba mu da jihar da ta fi ta, fitina barci take yi kuma Allah Ya la’anci mai tada ta. Mu mutane ne da Allah Ya bai wa shugabanci, duk wani mahaluki da ke wannan jihar yana da alhaki a kanmu, don haka ba za mu so a yi wani abu da zai tada hankali ba, ko mu maida martani ko mu tada fitina ba. Haka Mai daraja Gwamna ya ce, duk inda aka je, duk inda aka yi wani abu, kada wani ya dauki mataki, fada ne dai ba za a yi ba, kuma mutum ba ya fada shi kadai, ya ce in sun zo sun lalata kayayyaki Mai girma Gwamna da Sanata Ahmad Sani sun ce za a biya abin da duk aka lalata, fada dai ba za a yi ba.
Aminiya: Wai da gaske ne an kwace muku motoci?
Sani Gwamna: Wannan ba gaskiya ba ne, kuma duk inda muke tafiya babu inda aka ce an gwada jifar mu ma balle a ce an kwace mana mota, wani abu ma da ba ka sani ba shi ne komai dare duk inda muka je sai mun iske ana jirarmu mata da maza manya da yara kuma ko da karfe nawa ne.  
Aminiya: Amma a rediyo abokan adawa na yawan cewa idan kuka je kamfen har jifarku ake yi, mene ne gaskiyar magana?
Sani Gwamna: To,ni ban taba sanin wuri guda wanda aka yi haka ba.
Aminiya: Yaya kuke ganin karbuwar dan takararku na Shugaban kasa Janar Buhari a nan Jihar Zamfara?
Sani Gwamna: Idan kana neman dan Jam’iyyar PDP wanda bai san ciwon kansa ba, to ka kai karshe idan ka zo wannan jiha tamu ta Zamfara, duk Arewa babu jihar da za ka je ka samu cewa dan PDP yana kokarin ya zabi Shugaban kasa ba Buhari ba idan ba wannan jiha tamu, su kadai ne don ba su san ciwon kansu ba, Shugaban kasa dan PDP ne, amma kana jin abin da suke magana a kansa duk inda PDP suka je za su ce Najeriya za ka ji sun ce sai Buhari, amma a nan abin ba haka yake ba. A Kano da Jigawa da Kaduna da Bauchi da sauran wurare, sai Buhari ake cewa, wannan ka san karshen rashin sanin ciwon kai ne. Kowa ya san cewa Janar Buhari bai taba faduwa zabe a Jihar Zamfara ba balle yanzu da aka yi hadaka, ko a garin Shinkafi garin su Mamuda Shugaban kasa bai ci ba, balle yanzu da gwamnati ba ta hannunsa.
Aminiya: Idan na fahimce ka kamar a Kano da Kaduna da sauran wurare suna cewa PDP a jihohinsu za su yi, APC ne a sama su zabi Janar Buhari, amma a nan jihar ba haka yake ba?
Sani Gwamna: Su a gare su wadannan shugabannin ba, amma shi talaka ai ba shi da matsala, kuma a nan Jihar Zamfara ba su da talakawa, kowa ya sani, duk wanda yake Zamfara ya san PDP ba ta tare da talakawan Zamfara, an yi daya an yi biyu an yi uku an yi kuma a hudu, maganar kawai ita ce siyasar gidan rediyo ce.
Aminiya: PDP na cewa za su kawo wa Shugaba Jonathan kashi 25 cikin 100 a zabe mai zuwa me zaka ce?
Sani Gwamna: Ai ko kashi 3 cikin 100 ba za su kawo masa ba da izinin Allah, wannan magana siyasa ce domin su amso kudi daga wajensa don su zo su rika rushe gidajen mutane.
Aminiya: Kana cikin wadanda ake shiga lungu da sako da su don kamfe ko ka gamsu da yadda shugabannin jam’iyyarku ke gudanar da ayyukansu na yakin neman zabe?
Sani Gwamna: kwarai da gaske, domin da ni ake komai ina ganin yadda abubuwa suke gudana, kuma na ga yadda Mai daraja Gwamna yake dauko wasu alkawura kuma ya cika musu.
Aminiya: To a karshe yanzu wane kira kake da shi musamman ga ’ya’yan jam’iyyarku ta APC?
Sani Gwamna: Kirana shi ne duk yadda aka takale mu da fitina to kowa ya yi hakuri, akwai abubuwan da suka faru a baya wanda ba a ko bari ka manna fosta, amma ya zo ya wuce, kai  ba a ma bari ka ko gaisa da wanda jam’iyyarku ba daya ba, amma abin yanzu ya wuce, don haka hakurin da aka yi a baya shi ne zai ba mu nasara. Don haka ina kira ga ’yan jam’iyyarmu duk wanda aka yi wa wani abu, to ya yi hakuri kada ya tada fitina, wanda kuma ba zai iya hakuri ba, to ya kai wa hukuma tana nan.