Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya ce ’yan Najeriya suna rayuwar ƙarya kafin gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur, matakin da ya ce ya zama dole don hana ƙasar rushewa.
Tinubu ya yi wannan bayani ne, yayin bikin yaye ɗaliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure (FUTA), inda ya samu wakilcin Farfesa Wahab Egbewole, Mataimakin Shugaban Jami’ar Ilorin.
- Firimiya: Liverpool ta ci gaba da jan zarenta bayan doke Man City
- Mutum 4 sun rasu a hatsarin mota a hanyar Kaduna-Abuja
“Tallafin, wanda aka tsara don taimakon talakawa, ya zama yana cutar da su,” in ji shi.
“Rayuwar jin daɗin da muka ɗauka muna yi ba gaskiya ba ce domin tana iya kai ƙasar nan ga rushewa.
“Cire tallafin man fetur da karya darajar Naira matakai ne masu wuya, amma wajibi ne domin ceto makomar ’ya’yanmu.”
Shugaban ƙasar, ya kuma yi magana kan ficewa da matasan Najeriya ke yi zuwa ƙasashen waje, inda ya yi su daure su daina.
“Masana da ƙwararru da aka horar da su da dukiyar ƙasa suna barin ƙasa a lokacin da ake buƙatarsu fiye da kowane lokaci.
“Wannan ba ita ce mafita ba. Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa lokacin yin dariya na nan tafe. Mun himmatu wajen gina Najeriya mai cike da inganci,” in ji shi.
A wajen taron, Mataimakiyar Shugaban FUTA, Farfesa Adenike Oladiji, ta bayyana cewa ɗalibai 6,405 ne suka kammala karatu, ciki har da 519 da suka samu sakamako mafi kyau.
Ta kuma bayyana nasarorin da jami’ar ta samu a fannin koyarwa, bincike, da ci gaban al’umma.