’Yan Najeriya sun caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bayan ya zargi Gwamnatin Buhari bisa yawan daukewar wutar lantarki.
A ranar Laraba Atiku, dan takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya soki Gwamnatin Buhari kan katsewar lantarki a Najeriya baki daya.
- Zan karasa aikin da Buhari ya fara na cefanar da NNPC — Atiku
- Atiku ya yi raddi ga masu sukar sa kan kin daukar Wike a matsayin mataimaki
A sakon da Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya zargi Gwamnatin Buhari da gazawa a fannin lantarki inda a shekara guda an samu daukewar wutar a fadin Najeriya sau shida.
Ya bayyana cewa idan har ya zama shugaban kasa a 2023 zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya bunkasa bangaren wutar lantarkin domin farafado da tattalin arzikin Najeriya.
Wallafa sakon Atikun a shafinsa na Twitter ke da wuya, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar AAC, kuma babban mai sukar Buhari, Omeyele Sowere, ya yaza wanda ya fara caccakar sa.
Soweren ya zargi Atiki da rashin tabuka komai a lokacin da yake Mataimakin SHugabna Kasa, duk da irin makudan kudade da aka ware a bangaren a wancan lokaci.
Ya ce, “An fara samun daukewar wutar lantarki a fadin kasa tun a lokacin da kai da Obasanjo kuka kashe Dala biliyan 16 don jefa Najeriya a duhu.
“Buhari ya gaji wannan matsalar ne daga wurinku; Alhaji Atiku, kar ka fara tunanin nuna mana cewa ka damu da matsalar wutar,” a cewar Soweren.
Baya ga Soweren, daidaikun mutane ma sun yi wa tsohon mataimakin shugaban ca, da cewa ba wani abu da zai fada wa musu a kan wannan batu.
Sun bayyana cewa me ya sa tun a lokacin da su Atiku da Obasanjo ke kan mulkin sa ba su yi wata hobbasa ta kawo karshen matsalar wutar ba?
@bailonyeivene ya ce, “A shekaara takwas da Atiku ya yi a matsayin mataimakin shugaban kasa me suka yi a bangaren lantarkin?”
Har wa yau Rotimi @Rotimi360 ya yi , “Atiku ya kamata ka tuna cewa Dala biliyan 16 da aka kashe kan lantarki lokacin da kuke kan mulki, ’Yaradua da ya bincika lamarin bai tarar da komai ba.”
Matsalar lanatarki na daya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta da aka kasa shawo kai har yanzu duk da cewa gwamnatoci da dama sun yi yunkurin ganin bayanta, amma har yanzu abin yana cin tura.