Yan Najeriya da jami’an hukumar kwallon kafa ta Najeriya sun soki lamirin ka’idojin da hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta bi wajen zaben gwarzon kwallon Afirka ta bana bayan dan kasar Kwaddebuwa wanda ke kwallo a kulob din Manchester City da ke Ingila Yaya Toure ya lashe kyautar a makon jiya.
Masu horar da kungiyoyin kwallon kafa na kasashe 54 ne suka zabi ’yan wasa 10 da suka yi takara inda aka yi amfani da ka’idar kuri’a daya tana daidai da daraja 10 kuma duk dan wasan da ya sami daraja mafi yawa shi za su zaba.
dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Yaya Toure ya sami daraja 373 saboda masu horar da ’yan wasa na kasashen 28 sun kada masa kuri’a kuma sun zabe shi a matsayin wanda ya fi kowane dan wasa maki a shakarar da ta gabata wanda hakan ya sa ya zo na daya kuma ya doke abokan takararsa John Mikel Obi na Najeriya da kuma Didier Drogba da ya fito daga Kwaddebuwa.
Shi kuwa dan wasan kwallon kafa na kungiyar Chelsea da ke Ingila, Mikel Obi ya sami maki 275 ne don haka ya kasance na biyu.
Jim kadan bayan an bayyana Yaya Toure a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka na bana sai Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF)
Alhaji Aminu Maigari ya bayyana cewa ‘Ban ji dadin yadda Mikel bai lashe kyautar ba. Saboda haka dole mu sake yin nazarin ka’idojin da ake bi wajen zabar wanda ya lashe kyautar’.
Shi ma Alhaji Sani wani mai sha’awar kwallon kafa ya bayyana bakin cikinsa dangane da yadda aka bayyana Yaya Toure a matsayin wanda ya lashe kyautar.
Ya ce ‘Kamata ya yi a ce an ba Mikel Obi domin ya yi kokari kuma ya nuna bajinta fiye da wadanda suka yi takara tare musamman yadda ya samu nasarar lashe kofin Afirka a shekarar bara da kuma lashe kofin Europa a yankin Turai da kulob din Chelsea.
’Yan Najriya da dama da Aminiya ta tattauna da su jim kadan bayan an kammala bikin bayar da kyautar sun yi zaton Mikel Obi ne zai lashe kyauta kamar yadda tsohon dan wasan kwallon kafa na Arsenal Kanu Nwanko ya lashe a shekarar 1999.
’Yan Najeriya sun koka kan yadda aka zabi gwarzon dan kwallon Afirka na bana
Yan Najeriya da jami’an hukumar kwallon kafa ta Najeriya sun soki lamirin ka’idojin da hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta bi wajen zaben gwarzon …
