✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Najeriya sun ki aminta da rigakafin COVID-19 —NCDC

NCDC ta koka kan yadda mutane ke kaurace wa allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya

Darakta-Janar na Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC), Dokta Ifedayo Adetifa, ya ce ana fama da karancin mutane masu karbar allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar.

Dokta Adetifa ya bayyana haka ne ga manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, inda ya ce hakan ka iya haifar da koma baya ga kokarin gwamnati.

“Mutane ba sa zuwa yin allurar rigakafin Coronavirus, sannan duk an yi watsi da matakan kariya da aka shimfida don dakile ta.

“Yanzu haka akwai allurar rigakafin da za a iya yi wa kashi 50 cikin 100 na mutanen da ke bukatar ta, amma mutane sun ki zuwa a yi musu,” a cewarsa.

Tuni dai NCDC ta sanar da kamuwar mutum uku da sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 na Omicron, wanda ya soma bulla a kasar Afrika ta Kudu.

A satin da ya wuce ne gwamnati ta fara barazanar hana ma’aikatan da ba su karbi allurar rigakafin cutar ba shiga wuraren aikinsu.

Ko a makon nan mai karewa sai da aka hana wasu ma’aikata shiga wuraren aikinsu a Abuja.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta yi gargadi cewa sabon nau’in kwayar cutar na COVID-19, yana da hadari kuma yana iya kawo koma baya ga yaki da cutar da ake yi a fadin duniya matukar mutane ba su bi matakan da suka dace ba.