✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya Miliyan 6.3: Likita 2

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayar da sanarwar kafa kwamitin da zai binciki zargin da ake wa dan…

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayar da sanarwar kafa kwamitin da zai binciki zargin da ake wa dan kwallon Uruguay mai suna Luis Suarez a kan cizon da ya yi wa dan kwallon Italiya mai suna Giorgio Chiellini a karawar da suka yi a gasar cin kofin duniya a ranar Talatar da ta wuce.
A wasan, Uruguay ce ta doke Italiya da ci daya mai ban haushi, kuma hakan ce ta sa Italiya yin ban kwana da gasar.
Sai dai a lokacin da wasa ke gudana ne aka ga dan kwallon Italiya Giogio ya kama hannunsa yana ihu saboda cizon da Suarez ya yi masa ba tare da sanin dalilin yin hakan ba.
Kuma abin mamaki shi ne yadda alkalin wasan bai lura da cizon ba, don haka babu wani hukunci da aka yi wa Suarez.
Ganin yadda ba a hukunta Suarez a filin wasa ba kuma alkalin wasan bai ambaci cizon a rahoton bayan wasan da ya gatabatar wa Hukumar FIFA  ba ta sa hukumar yanke shawarar kafa kwamiti don yin binciken akan al’amarin.
Akwai yiwuwar a yi wa Suarez hukunci mai tsanani idan aka same shi da laifi.
An taba samun Suarez da laifin yin cizo har sau biyu a kasashen Holan da kuma Ingila a yayin kwallo inda aka yi masa hukunci daban-daban da suka hada da dage shi daga yin wasanni 6 da kuma 10 a lokuta daban-daban.
Sai dai akwai yiwuwar a yi masa horo mafi tsanani a wannan karon.
A gobe Asabar ne Uruguay za ta kece raini da Kolombiya a wasa zagaye na biyu.

Wasannin Gobe da Jibi
Asabar 28 Ga Yuni, 2014
Brazil da Chile            Biyar na yamma
Kolombiya da Uruguay     Tara na dare

Lahadi 28 Ga Yuni, 2014
Holan da Meziko        Biyar na yamma
Costa-Rica da Greece        Tara na dare