Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da saurasn masu ruwa da tsaki sun koka kan cewa akalla ‘yan Najeriya miliyan 14.3 ne ke ta’ammali da miyagun kwayoyin a fadin kasar.
Nau’in kwayoyin da aka fi amfani da su a cewarsu sun hada da tabar wiwi, hodar iblis, maganin tari na Kodin da dai sauransu.
Da take jawabi ranar Talata yayin wani taron yaki da miyagun kwayoyi tsakanin matasa wanda gidauniyar Baba-Rabi ta shirya a Abuja, Daraktar Sashen Rage Yawan Miyagun Kwayoyi ta NDLEA, Titus-Awogbuyi Joyce ta ce alkaluman hukumar sun nuna akwai akalla ‘yan Najeriya miliyan 14.3 masu shan miyagun kwayoyin a iya shekarar 2018 kawai.
Ta kuma ce alkaluman nasu sun nuna cewa mutum daya daga cikin kowane mutum hudu masu ta’ammali da kwayoyin mace ce.
A nasa jawabin, Minista a Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Clem Ikanade Agba, ya koka kan yadda amfani da kwayoyin ke kara zama ruwan dare tsakanin ‘yan Najeriya kusan a kullum.
Ministan wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa kan harkokin hulda da hukumomin gwamnati, Abdulrahman Na’ibi Rajab, ya ce hakan na matukar shafar cigaban kasa.
Ita kuwa shugabar gidauniyar ta Baba-Rabi, Nana Fatima Mede cewa ta yi kusan babu wani iyali da ya tsira daga matsalar miyagun kwayoyin a Najeriya.
Ta ce hakan ba zai rasa nasaba da yawan aikata laifuka da kuma karya dokokin hanya ba.