Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi ‘yan takara masu gaskiya da rikon amana a zaben shekarar 2019.
Shugaban wanda sakataren asusun kula da manyan makarantu (TETFund), Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya wakilta a taron Maukibi na mabiya darikar Qadiriyya da aka yi a karshen mako a Kano.
Shugaba Buhari ya ce, masu kada kuri’a suna da muhimmiyar rawar da zasu ta ka wajen yakar cin hanci da rashawa a duk matakan gwamnati.