Kungiyar likitoci ta Doctors Without Boarders ta ce ’yan Najeriya 90,000 ne suka kamu da cutar amai da gudawa a Najeriya shekarar 2021 da muke ciki.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’an Ofishin kungiyar a Najeria, Husseini Amri da Abdulkareem Yakubu suka fitar.
Sanarwar ta ce duk da cewa an samu wadanda suka kamu da cutar a ko’ina daga sassan kasar nan, amma abin ya fi kamari a yankin Arewa musamman jihohin Kano, Jigawa, Bauchi, Zamfara Sakkwato da Katsina.
An danganta hakan da yawan al’ummar da ke rayuwa a jihohin da yanayin rashin tsaron da ake fama da kuma rashin samun ruwan sha mai tsafta da alummar yankunan jihar ke fama da su.
Kungiyar ta ce a yunkurin ta na dakile yaduwar cutar ta bude cibiyoyin kula da cutar guda shida a wannan yankin kuma sun bawa mutane sama da 20,000 taimakon gaggawa.
Ko a watan Yuli, Cibiyar Kula da Cutuka ta Kasa ta ce akan samu wadanda su ka kamu da cutar sama da 7,500 a duk mako.