✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe ’yan Najeriya 693, an sace 494 a watan Agusta —Rahoto

An yi garkuwa da mutum 496 a cikin watan na Agusta.

’Yan Najeriya akalla 693 ne aka kashe, aka kuma yi garkuwa da wasu 494 a sassa daban-daban na kasar a watan Agustan 2021, a cewar rahoton Cibiyar Wanzar da  Zaman Lafiya a Yammacin Afirka (WANEP).

Alkaluman sun nuna fararen hula 674 ne aka kashe — ciki har da mata 23 da kananan yara 17 — sai jami’an tsaro 19.

Rahoton ya ce kashe-kashen Jihar Filato su ne mafiya muni a cikin watan, inda aka kashe mutum 122, sai Zamfara 121, Kaduna 111, Katsina 64, sai Neja 37; A Borno an kashe mutum 27, Imo 26, Ribas 24, Ogun 21, Binuwai 18, Delta 15, Osun 14, Legas 13, Ondo da Taraba bakwai-bakwai; A jihohin Oyo, Enugu da Kuros Riba kuma an kashe mutun dai-dai.

  1. Wadanda suka yi kisan

Daga cikin mutanen, ’yan bindiga sun hallaka ’yan Najeriya 177 a cikin watan, wasu mutum 183 kuma suka rasu a yayin artabu taksanin jami’an tsaro da ’yan ta’adda.

Sauran sun hada da mutum 173 da aka kashe a rikicin masu dauke da makamai, 96 a rikicin manoma da makiyaya, rikicin kabilanci kuma ya lakume rayuka 13.

An yi wa mutum 16 kisan gilla, kungiyoyin asiri sun kashe 15, mutum tara sun rasu a kazaman rikice-rikice.

Boko Haram ta kashe mutum uku, rikicin ma’aurata ya lakume rayuka biyu, an kuma kashe mutum a tarzoma.

  1. Garkuwa da mutane

Binciken ya gano an yi garkuwa da mutum 496, a cikin watan na Agusta.

Ciki wadanda aka yi garkuwar da su har da mata 37 da kananan yara 22 a hare-hare 66 da aka kai a jihohi 18.