✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya 350 da suka makale a Sudan sun hau jirgi zuwa gida

’Yan Najeriya kimanin 350 sun isa filin jirgi da ke Aswan a kasar Masar da misalin karfe 9.30 na safe.

’Yan Najeriya da suka shiga kasar Masar bayan yaki ya ritsa da su a Sudan suna hanyar dawowa Abuja.

Aminiya ta gano cewa ’yan Najeriya kimanin 350 sun isa filin jirgi da ke Aswan a kasar Masar da misalin karfe 9.30 na safe.

Majiyar ta ce, “Za a kwaso su a jirgin soji da na kamfanin AirPeace; 80 a jirgin soji samfurin C-130 sai wasu 274 a jirgin Airpeace.

“An fara hawa jirgi bayan an gama tantance su,” kafin su kamo hanya zuwa Abuja, inda ake sa ran za su iso bayan la’asar.

Majiyar ta ce wasu mutum 20 daga cikin fasinjojin kan iyakar kasar da ke Arqeen saboda rashin samu wuri a jirgi.