‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Jigawa hudu za su maka ta a kotu saboda cire su daga shugabancin kwamatocin da suke jagoranta ba bisa ka’ida ba.
Dan Majalisa Mai Wakiltar Gwaram kuma tsohon Kakakin Majalisar Idris Isah Gwaram ya sanar da haka a madadin Aminu Sule Sankara da Dayyabu Shehu Gwalo da Kuma Sani Isyaku.
Ya ce cire su da Shugaban Majalisar ya yi ya saba wa sashe na 118 na dokokin majalisar domin ba a sanar da su laifinsu ba a rubuce ko da baki kuma babu wata ka’ida da aka cika wajen cire su. Don haka tsanace da kiyayya da bi-ta-da-kulli majalissar da gwamnatin jihar suke musu.
A baya Isah Idris shi ne Shugaban Kwamatin Kula da Tsaftace Birnin Dutse (DCDA); Dayyabu Shehu Gwalo Kwamatin Amsar Korafe-Korafe; Isyaku Sani Gumel Kwamatin Agajin Gaggawa; shi kuma Aminu Sule Sankara Kwamatin Diddigi.
Amma yanzu shugaban majalisar ya umarci Hon. Sale Baba Buji da Hon. Jallo su rika kula da kwamatocin zuwa wani lokaci.
A jawabinsa Sani Isyaku ya ce kafin cire sun kamata ya yi a sanar da su sati daya kafin a gabatar da muradin a zauren majalisar sannan sai kashi uku bisa biyar na ‘yan majalissar sun zauna sun amince kafin a iya cire su. Ya ce saboda haka za su je kotu domin an cire su ne ba tare da wani dalili ba.
Sani Isyaku ya ci gaba da cewa maganar rashin kudi da majalisar ta ce take fuskanta karya ce domin gwamnatin jihar ba ta cire ko da sisin kwabo ba daga naira miliyan dari da goma da take ba majalisar a duk wata.
Ya ce cire su da a kayi abin kunya ne, cin fuska ne kuma abin Allah wadai ne kasancewar babu wata ka’ida da aka bi ko aka cika.