Wasu ’yan Majalisar Wakilai biyar sun sauya sheƙa daga jam’iyyar Labour Party (LP) zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulkin ƙasar.
Wakilan da suka bayyana sauya sheƙa a zaman majalisar na yau Alhamis sun haɗa da Esosa Iyawe (Jihar Edo), Tochukwu Okere (Jihar mo), Donatus Matthew (Jihar Kaduna), Bassey Akiba (Jihar Kuros Riba), Daulyop Fom (Jihar Filato).
- Uwargidan Zulum ta raba wa nakasassu 400 tallafi a Borno
- Jirgin mataimakin Zulum ya kama da wuta a sararin samaniya
Sai kuma Erhiatake Ibori-Suenu (Jihar Delta), wadda ’yar tsohon gwamnan jihar ce, James Ibori, da ita ma ta fice daga PDP zuwa APC ɗin.
’Yan majalisar sun ce rikicin shugabanci da jam’iyyar tasu ke fama da shi ne dalilin da suka fice daga cikinta.
Bayan shafe shekaru fiye da 20 tana gwagwarmaya a matsayin wani bangare na Ƙungiyar Ƙwadago, jam’iyyar Labour ta yi nasarar shiga fagen siyasar Najeriya a zaben 2023, inda ta samu kujerun sanatoci 6 da na ‘yan majalisar wakilai fiye da 34.
Ɗan takarar LP Peter Obi, shi ne ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da aka gudanar, abin da ya jawo wa jam’iyyar tagomashi karon farko cikin kusan shekara 20.