✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan majalisar tarayya 2 na PRP da APGA sun sauya sheka zuwa APC

Mambobin Majalisar Wakila guda biyu sun dangwarar da jam'iyyun da suka ci zabe a cikinsu zuwa jam’iyya APC mai mulki.

Mambobin Majalisar Wakila guda biyu sun dangwarar da jam’iyyun da suka ci zabe a cikinsu zuwa jam’iyya APC mai mulki.

’Yan majalisar sun hada da Yakubu Shehu Abdullahi na Jam’iyyar PRP dake wakiltar mazabar Bauchi a jihar Bauci da takwararsa, Blessing Onu ta APGA, mai wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini daga jihar Binuwai kuma diya ce ga tsohon Sugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.

Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da sauya shekar a zauren majalisar yayin zamanta na ranar Talata.

Abdullahi, tsohon dan jam’iyyar PRP, ya ce ya fice daga jam’iyyar tasa sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibayeta, lamarin da a cewarsa ya haifar da samar da shugabanni biyu a jiharsa ta Bauchi.

Dan majalisar ya ce, tun da farko sai da daya daga cikin tsagin shugabancin jam’iyyar masu fama da rikici suka rubuta takardar dakatar da shi daga cikinta.

Ya kuma ce rikicin ya rarraba kan mambobin jam’iyyar a kusan ko’ina a fadin jihar.

Ita kuwa a nata bangaren, Onuh ta ce ta yanke shawarar shiga jam’iyyar APC tun disambar 2020, ta kuma shirya gangami wanda ya tabbatar da ficewarta ta daga APGA zuwa APC.

Ita ma ta ce, APGA na cikin rikicin shugabanci a matakai daban-daban a jiharta, wanda hakan ya sa ta yanke shawarar tsunduma cikin APC.