Marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya sun taya Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden murnar zama shugaban kasarsa na 46.
’Yan majalisar sun kuma taya mataimakiyar Biden, Sanata Kamala Harris murnar zama mace ta farko bakar fata da ta yi nasarar lashe zabe a muhimmiyar kujerar.
- Shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa
- An yankewa ‘yan Najeriya 6 hukunci a Dubai kan zargin daukar nauyin Boko Haram
- Buhari ya umarci a shigar da masu yi wa kasa hidima shirin inshorar lafiya
Marasa rinjayen a majalisar sun bayyana haka ne a wata takarda da jagornsu, Ndudi Elumelu ya saka wa hannu a ranar Litinin.
Ya bayyana Joe Biden a matsayin kwararren masanin harkokin gudanar da gwamnati, mai cikakkiyar kwarewa kasancewarsa dan Majalisar Dattawan Amurka na shekara 38 kafin daga bisani ya zama Mataimakin Shugaban kasar tsawon shekaru takwas.
Ya kara da ana kyautata zaton gwamnatin Biden za ta kawo sabbin tsare-tsare a matsayinsa na shugaban kasa na 46 a Amurka.