✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Legas na cin abincin Naira biliyan 4 da rabi a kullum – Sanwo-Olu

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ce mazauna Jihar na cin abincin da ya kai na Naira biliyan hudu da rabi a kullum kwanan duniya.…

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ce mazauna Jihar na cin abincin da ya kai na Naira biliyan hudu da rabi a kullum kwanan duniya.

Ya bayyana hakan ne yayin taron bitar wayar da kai kan dabbaka dabarun sarrafa abinci  a Najeriya na kwanaki biyu a Legas.

Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta kasa da hadin gwiwar Ma’aikatun Noma da ta Tattalin Arziki da Kasafi da tsare-tsare ta Jihar Legas ne suka shirya taron.

A cewar Gwamnan ya ce Jihar na da tarihin habakar tattalin arziki da kuma samun sauyi mai amfani.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) kasa ya rawaito cewa Jihohin Oyo, da Ogun, da Ondo, da Osun da Ekiti na hadaka da Legas a matsayin jaha mai kula da yankin Kudu maso Yamma.

Gwamnan wanda Kwamishinan Tattalin Arziki, Tsare-tsare da Kasafi na Jihar, Sam Egube, ya wakilta, ya ce Jihar za ta jagoranci tabbatar da wadatar abinci ga mutanen da ke da mabanbantan hanyoyin noma da kiwo da sarrafa abinci a matakai daban-daban.

Ya ci gaba da cewa “Legas na da fiye da kaso 60 cikin 100 na masana’antu da harkokin kasuwanci, sannan Jiha ce da ke gabar ruwa wanda ya sanya ta ke da takaitattun filayen tsandauri, ban da kasancewarta gida ga mutane kimanin miliyan 21.

“Don haka abincin da mazauna cikinta ke ci a kullum ya kai na kusan Naira Biliyan hudu da rabi , da kuma kusan kaso 50 na naman Shanun  da ake sarrafawa a kasar nan, da ke kai wa na biliyoyin Naira zuwa wasu harkokin kasuwancin, da ake gudanarwa a fadin Kananan Hukumomin Jihar.”