✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Kwankwasiyya na son PDP ta kori Kwankwaso

Kusoshin Kwankwasiyya sun yi ganawar sirri da Sule Lamido suna son uwar jam'iyyar PDP ta kori Kwankwaso daga jam'iyyar

An samu baraka a tafiyar siyasa ta Kwankwasiyya, inda wasu kusoshinta a Jihar Kano suka bukaci uwar jam’iyyar PDP da ta kori Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar.

Mambobin Kwankwasiyyan sun bukaci Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP na Kasa ya soke rajistar Kwankwaso ne bayan wata ganawar sirri da suka yi da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, a ofishinsa da ke Kano ranar Talata.

Mambobin Kwankwasiyyar sun ajiye jajayen hulunansu, wadda ita ce alamar tafiyar, a lokacin zaman, wanda irin su Dokta Adamu Dangwani, Yusuf Danbatta, Akilu Sani Indabawa, da kuma mabiya bangaren Ambasada Ambassador Aminu Wali suka halarta.

Bayan ganawar, Sule Lamido a cikin sanarwar bayan taron mai dauke da sa hannun Yusuf Bello Danbatta, Akilu Sani Indabawa and Abdullahi Isa Sulaiman, na zargin Kwankwaso da yunkurin ci gaba da jan ragamar PDP, alhali kuwa yana kafa jam’iyyar adawa ta NNPP.

“Wannan yunkuri ne na yi wa PDP manakisa a zbaen 2023 da abin da zai biyo baya kuma manufarsa ita ce hana PDP tsayar da dan takara a 2023, ta hanyar amfani da jadawalin zaben da hukumar zabe ta fitar,” inji takardar da Dambattta ya karanto.

Takardar bayan taron ta ce barin ragamar PDP a hannun Kwankwaso a irin wannan yanayi tamkar sanya miliyoyin mambobi da mabiya jam’iyyar PDP a wani wadi mara bullewa ne.

A kwanakin baya ne dai Kwankwaso ya bude sabuwar tafiyar siyasa ta TNM, daga baya kuma ya sanar cewa zuwa karshen watan Maris zai sauya sheka zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP.

Tuni wasu mukarrabansa suka riga suka koma NNPP, amma ko a baya-bayan nan, ya dage cewa har yanzu shi dan jam’iyyar PDP ne.

Kwankwasiyya na daga cikin bangarorin siyasa biyu da ke ikirarin zama halastattun shugabannin jam’iyyar PDP a Jihar Kano.

Dambatta ya ce korar Kwankwaso a wannan lokaci na da muhimmanci tunda a ranar 1 ga watn Afrilu za a fara sayar da takardar neman tsayawa takara a zaben 2023.

A cewarsa, muddin ba a taka wa Kwankwaso burki ba, PDP na iya wayan gari ba ta da dan takara, sai dai NNPP ko ma wasu jam’iyyan su tsinci dami a kala.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Mai Magana da Yawun Kwankwasiyya, Kwamred Aminu Abdussalam, da kuma Sanusi Bature, wanda shi ne Kodinetan Sashen Sadarwar Kwankwasiyya, amma abin ya faskara.

Har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, dukkansu wayoyinsu a kashe.

Amma Shugaban Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kano,Shehu Sagagi, daga bangaren Kwankwaso kuma dan Kwankwasiyya, ya ce zaman da aka yi da Sule Lamido “soki-burutsu ne.”

Ya yi zargin cewa Sule Lamido ya dade yana neman yadda zai samu wani tasiri a jam’iyyar PDP a Jihar Kano, amma ba zai yi nasara ba.

 

Daga Sagir Kano Saleh da Clement A. Oloyede & Salim Umar Ibrahim (Kano)