Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, Hadimin na Musamman ga Gwamnan Kano, ya ce wasu ’yan bangar siyasa da yake zargin magoya bayan Kwankwasiya ne sun far masa tare da kwace masa wayar hannu.
Ta shafinsa na Facebook, Abubakar ya ce da yammacin ranar Lahadi ne hakan ta faru, inda ’yan dabar suka dora masa wuka a wuyansa, kafin su kwace masa wayar.
- Jami’ar Benin Ta Karyata batun janye yajin aiki
- Wane bangare ya fi samun kaso mai tsoka a kasafin 2023?
“’Yan Kwankwasiyya ne suka tare ni a Kofar Dan Agundi, suka yi min barazana da wuka suka kwace wayar hannuna da ke dauke da layina da aka san ni da shi.
“Na yi sa’a cikin yardar Allah ban samu wani mummunan rauni ba.
“Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da kare rayukanmu daga irin wannan mugun nufi,” in ji shi.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga bangaren Kwankwasiyya game da wannan zargi na Balarabe.
An dade dai ana zaman doya da manja tsakanin magoya bayana Ganduje da magoya bayan tsohonn uban gidansa kuma jagoran tafiyar siyasa ta Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaba kasa na Jam’iyyar NNPP.
A ranar Lahadi ne Kwankwaso ya kaddamar da ofishin yakin neman zabe na NNPP a Jihar Kano.