Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙi ta Nijeriya (EFCC) ta ɗora laifin yawan lalacewar babbar cibiyar wutar lantarki ta ƙasa a kan ’yan kwangila masu sayo kaya masara inganci.
EFCC ta ce jabun na’urorin samar da lantarki da ake amfani da su ne babban musabbabin ɗauke wutar da ta munana a baya-bayan nan.
Ta ƙara da cewa a shekaru 20 da suka wuce, manyan ayyukan da aika aikatawar a fannin samar da wutar a Najeriya bai fi kashi ɗaya bisa biyar na abin da aka tsara ba.
Shugaban Hukumar, Ila Olukoyede, ne ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar baƙuncin Kwamitin Majalisar Tarayya kan Yaƙi da Rashawa a ofishinsa.
- Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato
- DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci
Ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya gano ya cewa yawancin ’yan kwangilar da ke ake ba wa aikin samar na’urorin samar da lantarki a Nijeriya, ba mai inganci suke sayowa ba.
Ya ce, “idan kuka ga sakamako binciken da muka gudanar a ɓangaren lantarki sai kun zubar da hawaye.
“Ingancin na’urorin samar wuta da ’yan kwangilar suke sayowa bai fi rabin ingancin da ake buƙata na, shi ya sa wutar take yawan ɗaukewa ko kayan su ƙone, lamarin da ke jefa ƙasar cikin duhu.”
Wannan shi ne dalilin yawan lalacewar na’urorin da ke haddasa yawan ɗauke wutar a ƙasar nan, a cewarsa.
Olukoyede ya jaddada cewa babu inda a Nijeriya za ta je muddin aka ci gaba da amfani da kaya marasa inganci, musamman a muhimman ɓangarori kamar na wutar lantarki da sauransu.
Ya ce hukumar EFCC ta ƙudiri aniyar yin aiki tare da majalisar domin yi wa tufkar hanci.