✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon U-17 biyu sun koma Arsenal

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) Kelechi Nwakali da kuma takwaransa Samuel Chukwueze sun gama shirye-shiryen rattaba wa kulob…

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) Kelechi Nwakali da kuma takwaransa Samuel Chukwueze sun gama shirye-shiryen rattaba wa kulob din Arsenal na Ingila hannu kafin karshen wannan wata da muke ciki.
Rahotanni da suka fito sun nuna tuni ’yan kwallon suka ziyarci Ingila don kulla yarjejeniya da kulob din na Arsenal.
Rahoton ya nuna ana sa ran nan da karshen wannan watan ne a lokacin da ’yan kwallon biyu za su cika shekara 18 da haihuwa za su kulla kwantaragi da kulob din na Arsenal.
Wani kamfani mai suna Stellar Group wanda ya kware a cinikin ’yan kwallo ne ya zama dillalin ’yan kwallon. Haka kuma kamfani ne ya zama dillalin wadansu zaratan ’yan kwallo a sassan duniya.<br />Kelechi Nwakali ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon da ya fi nuna kwazo a gasar cin kofin duniya na matasa (U-17) da ya gudana a bara.<br />Ya taba ziyartar kulob din Manchester City na Ingila a bara amma kulob din bai dauke shi ba saboda ya riga ya kulla yarjejeniya da dan uwansa Chidiebere Nwakali.<br />Da ma can ya nuna ya fi sha’awar yin kwallo a kulob din Atrsenal musamman ganin yadda ’yan kwallon suke lailaya kwallo da hakan ta sa ra’ayinsa ya fi karkata zuwa kulob din sai ga shi yanzu mafarkinsa ya zama gaskiya.