’Yan kwallon kulob din Sunshine Stars da ke Akure na Jihar Ondo sun fara yunkurin tafiya yajin aiki muddin mahukunta kulob din ba su yi wani abu a kan bashin albashin da suke bi na wata da watanni ba.
’Yan kwallon sun koka game da yadda suka shafe kimanin watanni bakwai ba tare da an biya su ko sisin kwabo ba. Don haka suka dibar wa mahukunta kulob din zuwa ranar 30 ga wannan wata idan ba a biya su ba to za su tsunduma cikin yajin aikin sai baba-ta-gani.
A bara ne tsohon shugaban kulob din Akin Akinbobola aka ruwaito ya yi watsi da ’yan kwallon a lokacin da ya lura kulob din ba zai kai labari ba a gasar rukunin firimiya ta kasa abin da ya sa aka daina biyan ’yan kwallon albashi da kuma alawus-alawus dinsu. Sai dai bayan an samu canjin sababbin shugabanni su ma ba su yi wani yunkurin ganin sun biya ’yan kwallon hakkokinsu ba.
daya daga cikin ma’aikatan kulob din wanda ya ki amincewa a ambaci sunansa jim kadan bayan kulob din ya lallasa na El-Kanemi da ci 1-0 a ranar Lahadin da ta wuce ya ce, kimanin watanni bakwai kenan rabon da a biya su albashi da hakan ya jefa su cikin mawuyacin hali.
“Iyalanmu ba sa ganinmu da daraja saboda mun kasa samar musu da abinci da bukatun yau da kullum saboda rashin biyanmu albashi amma abin mamaki mahukunta kulob din suna son mu rika samun nasara a wasannin da muke yi, ta yaya kake jin hakan zai iya faruwa?.
’Yan kwallon Sunshine Stars za su shiga yajin aiki
’Yan kwallon kulob din Sunshine Stars da ke Akure na Jihar Ondo sun fara yunkurin tafiya yajin aiki muddin mahukunta kulob din ba su yi…