✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Kamaru sun Musulunta a Dubai

Wani kulob da ke yin kwallo a rukunin ’yan dagaji (amateur) da ya fito daga Kamaru kuma ya kai ziyara Dubai don samun horo, daukacin…

Wani kulob da ke yin kwallo a rukunin ’yan dagaji (amateur) da ya fito daga Kamaru kuma ya kai ziyara Dubai don samun horo, daukacin ’yan kwallonsa da jami’an da ke horar da su sun musulunta  kamar yadda jami’an kulob din suka sanar.
Kafar sadarwar Gulfnews.com ta kalato cewa daukacin ’yan kwallon da jami’an sun musulunta ne saboda irin kyakkyawar tarbar da wata cibiya mai kula da marayu da gajiyayyu da ke karkashin addinin Islama mai suna (Islamic Affairs and Charitable Actibities Deparement (IACAD)  ta yi musu, bayan sun kai ziyara cibiyar.
daukacin ’yan kwallon da jami’an nasu sun musulunta ne a harbar cibiyar inda suka karbi shahada a lokaci guda.
Cibiyar ta ce ’yan kwallon sun karbi musulunci ne saboda irin kyakkyawar tarba da kulawar da suka samu a lokacin da suka ziyarci cibiyar, kamar yadda Daraktan cibiyar Dokta Hamad Ali Shaibani ya sanar.
Ita dai cibiyar takan shirya tarurrukan fadakarwa ga Musulmi da kuma wadanda ba Musulmi ba ne a duk shekara kuma takan gayyato kungiyoyi daban-daban daga sassan duniya daga lokaci zuwa lokaci.  
A kwanakin baya ne ta gayyaci matasan ’yan kwallon Kamaru a lokacin da suka ziyarci Dubai kuma hakan ne ya janyo hankalin  ’yan kwallon da jami’ansu shiga addinin Musulunci.
Cibiyar tana shirya tarurrukan fadakarwa a wurare daban-daban da suka hada da makarantu da manyan shaguna sayayya da kuma  wuraren nuna al’adun gargajiya.
A halin yanzu cibiyar na kula da cibiyoyin da ke karantar da addinin Islama guda 17 da kuma makarantun haddar Alkur’ani guda 38 a sassan duniya.