Magoya bayan kulob din Kaduna United sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta yi wa Allah ta biya basussukan albashin watanni 11 da ’yan kwallon kulob din da kuma masu horar da su ke bi bashi ba tare da bata lokaci ba.
Abdullahi Yusuf, jami’i mai kula da jin dadin kungiyar magoya bayan kulob din ne ya shaida wa manema labarai haka a Kaduna a karshen makon jiya.
Ya ce yin haka ne kadai zai ceto kulob din daga fadawa tarkon koma baya (relegation) a kakar wasa ta bana inda yanzu haka kulob din ne yake a matsayin na 18 daga cikin jerin kungiyoyin kwallon kafa 20 da ke fafatawa a gasar rukunin Firimiya ta kasa.
Ya ce rashin biyan albashin ne ya jefa ’yan kwallon cikin matsala na rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a kakar wasa ta bana.
“Ba zai yiwuwa dan kwallon da bai ci abincin kirki ba ya yi maka wasa yadda ya kamata, idan aka lura su ma ’yan kwallon mutane ne kamar kowa ta yaya za su samu kwarin gwiwar yin wasa alhalin suna fama da matsalar rashin kudi?”.
“Ina kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Ramalan Yero ya yi kokarin ceto kulob din Kaduna United daga halin taskun da yake ciki don kulob din kadai yake wakiltar jihar a gasar rukunin firimiya”.
“Yakamata gwamnan ya yi bincike akan yadda mahukunta kulob din suke gudanar da al’amurransu don gano bakin zaren”, inji Abdullahi Yusuf.
Sai dai kocin Kaduna United Saleh Barnabas ya ce nasarar da suka samu a wasan da kulob din ya yi a gida a kwanakin baya hakan ta faru ne a bisa sadaukarwar da ’yan kwallon suka yi duk da matsalar rashin albashin da suke fuskanta.
Ya zuwa wannan lokaci, Kaduna United ce take matsayin na 18 inda ta hada maki 30 daga cikin wasanni 25 da ta yi. Za ta yi wasanta na gaba ne da kulob din Heartland da ke Owerri.
’Yan kwallon Kaduna United suna bin bashin albashin watanni 11
Magoya bayan kulob din Kaduna United sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta yi wa Allah ta biya basussukan albashin watanni 11 da…